Kungiyar Darul Naharatul Ahababul Qur’an ta Kasa: Ziyarar Aiki da Tattaunawa da Hukumar Tsangaya

A ranar 19 ga Agusta, 2024, Kungiyar Darul Naharatul Ahababul Qur’an ta kasa, bisa jagorancin mai martaba sarkin Macina, Alh. Dr. Bashir Albishir Bukar Mai Machinama OON, L’ONN, ta sami gayyata daga Hukumar Kula da Nazarin Larabci da Addinin Musulunci (Center for Tsangaya and General Studies) karkashin Hukumar Kasa mai kula da Nazarin Larabci da Addinin Musulunci (NBAIS). An gudanar da wannan taro ne don tattaunawa da shugabannin kungiyar tare da jin tsare-tsare da manufofin kungiyar, da kuma duba hanyoyin inganta karatun Tsangaya da kawo karshen barace-barace da Almajirai ke yi a kasuwanni da gidaje.

A cikin jawabinsa, shugaban kungiyar Darul Naharatul Ahababul Qur’an ta kasa, Gwani Usman Muktar Muhammad Ladanai Hotoro, ya bayyana shirye-shiryen kungiyar na tallafawa Almajirai ta hanyoyi da dama. Cikin abubuwan da suka hada sun kasance:

  1. Tallafawa Almajirai da kayan makaranta,
  2. Samar da kayan karatu,
  3. Koyar da sana’o’in zamani,
  4. Samar musu da dakunan kwana,
  5. Samarmusu da bandakuna,
  6. Tallafawa rayuwar Almajirai da malaman tsangaya ta kowanne bangare don inganta ilimin addini a kasa baki daya.

Gwani Usman ya kuma jaddada muhimmancin yiwa kasa addu’a domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da tabbatarda cewa tattaunawar ta kasance mai fa’ida ga ci gaban ilimin addini da rayuwar Almajirai a kasar.

A nasa jawabin, babban darakta na Center for Tsangaya and General Studies, Dr. Ibrahim Lawal Kaura Zariya, ya nuna farin cikinsa da jin dadin ziyarar da uwar kungiya ta kaiwa hukumar. Ya bayyana cewa, hukumar an kirkireta ne domin taimakawa Almajirai da malaman tsangaya. Har ila yau, ya jaddada cewa tsare-tsaren Kungiyar Darul Naharatul Ahababul Qur’an ta kasa sun yi daidai da tsarin hukumar daga dukkan fannoni. Dr. Kaura ya kuma bayyana cewa, hukumar tasu ta bullo da wata sabuwar manhaja ta koyar da malaman tsangaya tare da basu takardar shaidar kasa (certificate) wanda zai baiwa malamai ko Almajirai damar shiga cikin tsarin gwamnati.

Zaman tattaunawar ya samu halartar manyan shuwagabannin sassa na hukumar, inda aka gudanar da muhimman tattaunawa da zai taimaka wajen inganta rayuwar Almajirai da malaman tsangaya a Najeriya.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *